Kungiyar Kurame Mai zaman kanta ta Karamar Hukumar Ning ta sake nada membobinta a yayin da aka za6i shugabani na Kowacce shiyya, Iyayen kungiyar da masu Ruwa da tsaki sune suka yanke Shawarar wanda ya kamata a nada na kowanne mukami.
Nadin dai ya gudana ne ranar Juma’ar data gabata a harabar tsohon Ciyaman a Unguwar tsamiya da ke Karamar Hukumar Ningi Jihar Bauchi.
Jaridar INN ta ruwaito cewa Idan shi tsohon Ciyaman Hassan Shehu ya kasance a matsayin wanda ya jagoranci Kungiyar ya kasance shugaban Kwamitin za6e da gudanarwa. Bayan an kamalla nadawa Shugaban Kwamitin ya ayyana Sunan Wanda aka za6a da zasu jagoranci Kungiyar har zuwa lokacin da ya kamata a sake nada sabbi ko ayi sabon za6e.
Jim kadan Bayan gamawa shugaban Kwamitin ya mika jagoranci Kungiyar ga sabon Shugabanta Dayyabu Shehu Ranga Wanda shine aka za6a a matsayin sabon Ciyaman, sai Kuma aka za6i Umar Saleh Burra Daga yankin Burra a matsayin mataimakinsa.
Sauran wadannan aka za6a sun hada da Jibrin Abdullahi a matsayin sakatare, Saleh Alh Shehu mataimakin sakatare Sai Auwalu Ladan a matsayin Mai hada kudaden kungiya da sauransu.
Sabbin Shugabanin sunyi Alkawarin Kawo Sauyi ga kungiyar domin kaita zuwa mataki na gaba domin ci gabanta, da Kuma al’ummar da take wakilta.
