Home Disability NewsHukumar NCPWD Zata Samar da Bangaren Taimakawa Na Fasahar Zamani

Hukumar NCPWD Zata Samar da Bangaren Taimakawa Na Fasahar Zamani

by Inclusive News Network
Published: Updated:

By Yusuf Mohammed Lawan, Gombe

Hukumar kula da harkokin masu bukata na musamman wanda akafi sani a turance da ‘National Commission for Persons with Disabilities (NCPWD)’ ta fara shirye – shiryen samar da wani bangare a farfajiyar hukumar da zai tamaka wajen tafiyar da abubuwan fasahar zamani a harabar helkwatar hukumar dake babban birnin tarayya Abuja

An bayana hakane yayin da babban sakataren hukumar NCPWD Dr. James David Lalu, PhD, npom, yake zanatawa da masu kawo sauyi a harkar fasaha a dai -dai lokacin bikin murnar zagoyowar ranar taimakawa fasaha ta duniya ranar 4 ga watan yuni, 2024.

Zaman zantawar ta bawa masu kawo sauyi kan harkar fasaha daman nuna kwarewar aikinsu da tsare-tsaren dasuka shirya don kawo sauyi mai muhimmanci da zai kawo cigaban aikinsu. Sabon bangaren taimakawa na fasahar zamanin zai dauki nauyin kulawa da gudanarwa gami da tabbatar da Samar da mafita ga duk matsalolin da zai shafi taallafin tsare -tsaren fasaha, tare da mai da hankakali sosai kan cigaban kere-keren cikin gida.

A wata sanarwa wanda da shugaban bangaren sadadarwa na hukumar Saleh Faruq Gagarawa, ya rattaba hannu, yace “wannan shiri yana daya daga cikin cikin kudurorin muradun karni guda takwas (8) wanda Dr. Lalu ya dukufa aiki akansu don cimma manufar hukumar na kawar da duk wata wariya da al-ummar masu bukata ta musamman ke fuskanta, muamman kudiri na biyu wanda take neman sanya taimakwa fasaha a mastayin abu mafi riba da muhimmanci a Najeriya.

Ya kuma kara da cewa “Hukumar NCPWD ashirye take da tayi aiki tukuru don ganin tayi duk abunyi da zai farfado da darajar rayuwar masu bukata ta musamman ta hanyar yin amfani da tallafin fasahan zamani da mai da hankali kan fasahohin kere-keren cikin gida”

Leave a Comment

* By using this form you agree with the storage and handling of your data by this website.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

You may also like

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Adblock Detected

Please support us by disabling your AdBlocker extension from your browsers for our website.