By Yusuf Mohammed Lawan,
Al-ummar nakasassun jihar Borno sunyi kira da babban murya ga gomnatin jihar da ta sakasu cikin harkar koyar da ilimin zamani na dijital da gomnatin ke gudanarwa kwanan nan, Wanda cibiyar cigaban fasaha da hada-hadar sadarwa mallakar jihar wato ” Borno State Information and Communication Technology Development Agency (BICTDA)”. Ke kaddamarwa a fadar jihar.
Nakasassun sunyi kiran ne ta wata sako da suka sanar ranar asabar da ta wuce inda suka zayyana bukatunsu na neman samun cikekken daman moriyar bunkasa harkar ilimin dijital na jihar.
Dayake tofa yawun bakinsa akan batun, shugaban kungiyar nakasassun Mal. Mohammed Abubakar Kwalwakwalwa, ya yabawa Gomnan jihar Prof Babagana Zulum da irin namijin kokarin da yayi na samar da cibiyar tare da nada Engr. Muhammed Ahmad Kabir Wanori a matsayin babban sakataren cibiyar na farko.
Engr. Muhammed Ahmad Kabir Wanori, babban sakataren cibiyar ya jaddada cewar tuni gomna Zulum ya riga ya amince da ware wa nakasassun jihar waje na musamman a duk cibiyoyin cigaban fasahar sadarwa ta jihar, a cewar sa hakan yana nuni da kulawar gomnatin wajen tabbatar da adalci ga kowa da kowa batare da nuna wariya ba
Ya kuma bukaci nakasassun da su bashi sunayen membobin kungiyar daga kowace karamar hukamar jihar don ganin ba’a bar kowa a bata ba wajen tafiyar ilimin fasahar sadarwa ta dijital a fadin jihar.
INN ta ruwaito cewa wannan hadin kan da aka kulla tsakanin nakasassun jihar da gomnatin jihar an kulla ne don inganta jin dadin rayuwa da bawa nakasassun jihar cikekken daman shiga dukkan harkokin cigaban tattalin arzikin jihar Borno.
