Daga Yusuf Mohammed Lawan, Gombe
Shugaban karamar hukumar Dukku dake jihar Gombe Hon. Muhammad Adamu Waziri, ya bawa zabebbiyar kansila Kurma Hon. Hauwa Saidu wanda akafi sani da suna Hajiya Ummi kuma wacce take wakiltar yankin Waziri ta arewa mukamin kansila mai kulawa da harkokin gudanarwa da sha’anin kudin yankin Waziri ta Arewa, na karamar Hukumar Dukku.
An sanar da bada mukamin ne ranar biyu ga watan Maris, 2024 cikin wata wasika dake rattabe da sa hannun Mal. Abubakar Hayatu a madadin Shugaban karamar hukumar.
Wasikar ta ruwaito kamar haka: “‘an umarce ni da rubutawa gami da tabbatar da jaddada amincewar baki mukami a matsayin mai kulawa da harkokin gudanarwa da sha’anin kudin yankin Waziri ta Arewa, karamar karamar Dukku ”
“Duk da cewa Shugaban karamar hukumar ya tabbatar da zakiyi aiki tukuru don sauke nauyin hakkokin ofishin dake kanki; burinmu shine zaki amshi wannan karamci da girmamawa da aka mini”
“A madadin mahukunta da daukacin al-ummar karamar hukumar Dukku, muna tayaki murnar samun wannan mukamin kuma muna adduar Allah ya shige miki gaba wajen gudanar da ayyukanki cikin lafiya, amin”